Kimanin tan dubu 70 na hatsi ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umurnin rarrabawa ma mabukata a jihar Lagos da Ogun da Abuja, da kuma wasu sassan kasar da ke bukatar tallafi.
Sakataren Gwamnati Boss Mustapha ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke cigaba da bayyana irin matakan da mahukuntan kasar ke dauka wajen magance yaduwar cutar Coronavirus.
Tuni ma Gwamnatin Najeriya ta fara bada tallafi ga masu karamin karfi wanda har wa yau shugaba Muhammadu Buharin ne ya bada umurnin haka, wanda aka fara daga karamar hukumar Kwali ta Birnin Tarayya ta hannun Ministar Ma'aikatar Jinkai, Sadiya Umar Farouq wacce ta ce ana da rajista da ke dauke da sunayen wadanda aka rarraba wa kudin.
Shamsiya Abdullahi tana daya daga cikin rukunin farko wadanda suka samu dubu ashirin kuma ta bayyana wa Muryar Amurka irin farin wikin da take ciki.
Shi ma tsohon Ministan Matasa da Wassani, Barista Solomon Dalung ya ce ya yaba da yunkurin, sa'annan ya yi kira ga masu hannu da shuni da su fito kwansu da kwarkwatansu su kawo wa kasa tallafi domin dakile yaduwar wannan annoba ta Coronavirus.
Saurari wannan rahoton a sauti.
Facebook Forum