Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Za a Je Zagaye Na Biyu a Zaben Shugaban Kasa


Mataimakin Shugaban CENI, Dr. Aladoua Amada
Mataimakin Shugaban CENI, Dr. Aladoua Amada

Hukumar zabe ta CENI a Jamhuriyar Nijar ta ce babu dan takarar da ya samu kashi 51 na kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 27 ga watan Disambar bara.

Hakan a cewar, mataimakin shugaban hukumar ta CENI Dr. Aladoua Amada, na nufin sai an je zagaye na biyu.

Hukumar ta ce, dan takarar jam’iyya mai mulki ta PNDS Mohamed Bazoum ya samu kashi 39.33 yayin da Mahamane Ousmane na RDR ya samu kashi 16.99.

“Kamar yadda kundi ya tanada, idan kana so ka wuce gaba daya, sai ka samu kashi 51 cikin 100, kuma alkaluman da muka fitar babu wanda ya samu wannan. Kenan muna tsammanin za a je zagaye na biyu kenan na shugaban kasa.” In ji Dr. Amada.

Hukumomin sun saka ranar 21 ga watan Fabrairu a matsayin ranar yin zaben a zagaye na byiu.

Tarihin dai ya nuna cewa rabon da wani dan takara ya samu nasara a zagayen farko, tun a shekarar 1993.

Yau Asabar aka gudanar da bikin sanar da sakamakon zaben na wucin gadi a babban dakin taro na Palais De Congres da ke Yamai, babban birnin kasar ta Nijar.

Tun a ranar Juma’a wa’adin da doka ta ba hukumar na tattara alkaluman zaben ya cika, inda hukumar ta ce ta gama komai illa ba da sakamakon zaben na wucin gadi.

Mataki na gaba shi ne, CENI za ta mika sakamakon ga kotun tsarin mulkin kasar wanda zai yi nazari akai sai ya sanar da shi a hukumance.

Kotun na da kwana 28 ta kammala wannan aiki.

Duk wani mai korafi kan sakamakon na da wa’adin kwana goma ya gabatar da kokensa daga ranar da aka mika sakamakon ga kotun.

Wannan biki na sanar da sakamako ya tattaro jakadun kasashen waje, wakilan jam’iyyu, sarakunan gargajiya, ‘yan sa ido na ciki da waje da kuma ‘yan jarida na ciki da na kasashen ketare.

A bangaren zaben ‘yan majalisar dokokin kasa ma jam’iyar PNDS mai mulki ke kan gaba da kujeru kimanin 80 daga cikin 166 sai Moden Lumana mai kujera 19 yayin da MPR Jamhuriya ta MNSD NASARA kowace ta sami kujera 13 jam’iyar CPR INGANCI na da kujera 8 sannan RDR Canji na da kujera 7.

XS
SM
MD
LG