Mataimakin shugaban hukumar Dr Aladoua Amada ne ya bayyana haka a hirarshi da Muryar Amurka.
Wannan na nuni da cewa, akwai yiyuwar fitar da kammalalen sakamakon zaben da aka gudanar ranar lahadi 27 ga watan Disamba a gobe juma’a 1 ga watan janerun 2021.
hukumar-ceni-na-ci-gaba-da-tattara-sakamakon-zaben-nijar
an-gudanar-da-zabe-mai-inganci-a-jamhuriyar-nijar---cen-sad
yadda-shugaba-issoufou-bazoum-ousmane-suka-kada-kuri-unsu
Maitaimakin shugaban hukumar zaben ya bayyana cewa, i zuwa lokacin yin wannan hirar sun kallama tattara sakamakon zaben gudumoni 151, watau ke nan cikin gundumomi 266 sauran 105, kuma sauran wadannan da suka rage duka sun riga sun shiga hannun hukumar zabe, abinda ake jira kafin wallafa sakamakon shi ne a tantance shi kafin sanar da shi a kafofin sadarwa da suka hada da radiyo da talabijin na kasa.
Mataimakin shugaban hukumar Dr Aladoua Amada ya ce, bisa ga dokar kasa, bisa kudurin doka na 156, hukumar zabe tana da kwana biyar ta wallafa sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa, ta sanar da al'umma sakamakon zaben, ta wallafa shi kuma ta mika sakamakon zaben ga kotun koli mai kula da harkokin zabe.
Ya kuma kyautata zaton cewa, za a fitar da wannan samakon zaben domin 'yan kasa a duk inda suke da kuma duniya su sani.
Mataimakin shugaban hukumar zaben ya musanta cewa sun sami tsaiko a gudanar da aikin. Bisa ga cewarshi, suna fitar da samakon zaben ne bisa ga lokacin da suka same shi.
Saurari cikakkar hirar Mataimakin shugaban hukumar Dr Aladoua Amada da wakilin Sashen Hausa Souley Mummuni Barma.