A jamhuriyar Nijar hukumomin kasar sun bada somacin neman a kama kakakin majalisar dokokin kasar Hama Amadou, kan zargin yana da hanu a fasakorin jarirai.Jami’an kasar suka ce wani alkali ne ya bada sommacin cewa a kamo kakakin majalisar domin ya amsa tambayoyi.
Hama Amadou, wanda yana daya daga cikin shugabannin ‘yan hamayyar kasar, cikin watan jiya ne ya tsere zuwa Faransa bayan da majalisar dokokin kasar ta bada umarnin a kama shi.
Hamma dai bai amince da zargin ba, yace bita-da-kullin siya ne. Mukarrabansa a majalisar dokokin kasar suka ce kama shi zai keta rigar kariya da yake dashi.
Tuni aka kama wasu mutane 17 kan wannan zargi ciki harda da ministan aikin noma, Abdou labo.
Ahalinda ake ciki kuma, Amurka ta bada Karin gudumawar dala milyan 83 a matsayin agajin gaggawa domin tallafawa ‘yan gudun hijira daga Sudan ta kudu.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce sabbin kudaden za a yi amfani dasu wajen sayen abinci, kiwon lafiya, samar da iri da kayan noma. Da wannan sabon kudin, adadin tallafin da Amurka ta bayar ga Sudan ta kudu a bana yah aura dala milyan dari bakwai da ashirin.