Ayar doka mai lamba cisi’in da daya ta kundin tsarin mulkin janhuriyar Nijer mai ci yanzu ita ta tilastama ‘yan majalisun Dokokin yin zaman taro har sau biyu a shekarar, inda yan majalisar ke duba halin da kasa ke ciki tare da jefa kuri’a akan sabon kasafin kudi na shekara mai zuwa.
To amma wata sabuwa ta sake barkewar, ‘yan majalisun sun sami kira har sau biyu, daga bangaren shugaban majalisar dokokin mai gudun hijara Malam Hama Amadou. Inda shugaban ya kira ‘yan majalisar Dokokin da su zauna ran bakwai ga wata mai hawa. Yayinda dayan bangaren kuma Sakateriyar fadar ta kira ‘yan majalisar Dokokin taro ranar daya ga watan gobe.
Wakilin muryar Amurka a Nijer Abdoulaye Mamane Amadou ya tuntubi shugaban rukunin ‘yan majalisar Lumana Afrika ta malam Hama Amadou mai adawa, Malam Bukar Yasaidu Sangare ya tabbatar da aika takardar kiran taron da shugaban majalisar yayi a zauren majalisar.
Wakilin muryar Amurka ya ce sai da yai tattaki har zuwa zauren majalisar, bai zame ko’ina ba sai Ofishin karbar takardu inda jami’ai suka fada masa cewa har yanzu basu sami wata takarda ba daga Ofishin shugaba Hama Amadou ta kiran taron majalisar ranar bakwai ga watan gobe. Sakataren ma ya kara tabbatar masa da cewa ba ya da wata masaniya akan takardar.
Amma a ta bakin honarable Saleh Hassan Amadou, dan jam’iyyar lumana Afrika mai adawa, yace batun ba haka yake ba.
A nasa bangaren, Ben Omari Mohammed mataimakin na hudu na shugaban majalisar dokokin ya jaddada cewa kiran taron na ran daya ga watan gobe shi ne akan ka’ida, ya kuma kara da cewa, muddun kotu bata wanke Malam Hama Amadou ba, yana nan a matsayin mai gudun hijira ne.