Wasu matasa a unguwa Jagindi da ke Damagaram na Jamhuriyar Nijar sun kudiri aniyar yakar sauro da ya zamo annoba wajen yada cututtuka, da yanzu haka al'umma suka cika asibitoci a Damagaram sanadiyar zazzabi da ya addabi jama'ar.
Maminu Malam Ado shi ne jagoran wadannan matasan, ya kuma ce su da 'yan uwa da abokanan arziki suka zauna su ka yi shawara yadda za su tasamma lamarin, inda su ka hada kudade su ka sayi injin din feshin da magani su ke fesawa a gidaje, unguwanni da wajen da sauro ya tare.
Wasu da suka ci moriyar wannan tsari sun ce ba karamin dadawa 'yan unguwar ya yi ba, inda mazauna unguwannin suka ce yanzu haka sauro ya yi sauki sosai.
A cewar jagoran matasan, za su fadada aikin feshin maganin har sauran unguwani da su ke kusa da su, sannan yana kuma kira ga sauran 'yan uwansu matasa da su yi koyi da su, wanda ta haka ne za a rage radadin zazabin cizon sauro da al'umma ke fama da shi, abin da ya kai asibitoti suka cika makil da marasa lafiya.
Saurari cikakken rahoton Tamar Abari daga Damagaram:
Facebook Forum