A hirar su da wakiliyar Muryar Amurka Tamar Abari, Abdu Bukari dan yankin, yace farar tana da yawa, kuma hatsi a wajen bai kai inda za a yanke shi, jama'a basu shiga wahala ba.
Yace suna bukatar agajin gaggawa daga hukumomin gidan gona, da na
kashe kwari, don kar matsalar ta kaisu shiga wani hali na tagayyara.
A nashi bayanin Darakta na hukumar gidan gona na Tanut, Lawali Bukari, yace tun watan baya ne suka fara ganin fara suka sa mata magani, yanzu kuma suka sake samun labarin ta dawo, amma tuni suka fara daukan matakin sanya magani a wuraren da take.
Daraktan ya ci gaba da cewa idan kuma fara ta matsa, akwai jirage masu
feshin magani da za'a yi amfani dasu. Yace yanzu dai suna kan aiki, ba za su bari ba, har sai sun kauda wannan matsala, saboda Damagu ita ce rumbun tsumin Nigar a fannin samar da wadataccen anfanin gona, don haka hukumomi suye tsaye don magance matsalar.
A saurari cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Tamar Abari.
Facebook Forum