Dama a kowace shekara masu fada a ji su kan yi taron gabanin fara azumin domin daukan alkawarin kauracewa kara farashin kayayyaki domin kada a muzgunawa al’uma.
A irin wannan lokaci akan samu ‘yan kasuwa da ke amfani da watan na azumi wajen kara farashin kayayyakin masarufi domin a lokacin ne magidanta suka fi shiga kasuwanni domin sayen musamman kayan abinci.
To sai dai wasu magidanta a Jamhuriyar ta Nijar, sun nuna shakkunsu dangane da wannan matsaya da ‘yan kasuwar suka dauka domin a cewar su ba dukkanin ‘yan kasuwan ne su ke bin umurnin ba.
Domin jin karin bayanin kan wannan batu, saurari rahoton wakilin Muryar Amurka, Sule Mumuni Barma daga Yamai: