'Yan jarida suna bada dalilai daban daban, wasu ma suna karo da juna shi ya sa ya ja kunnuwansu tare da cewa basu tsayar da dalili daya ba. Suna duba duk dalilan da ka iya haddasa hadarin.
Saboda haka ya rokesu kada su kama wani dalili takamaimai su ce shi ne sanadiyar faduwar jirgin. Wannan kalamun na shugaban shi ne na farko da zai yi tun lokacin da hadarin ya faru.
Yayinda yake yiwa ministoci da 'yan majalisar kasa jawabi a wurin bude wata ma'aikatar sarafa taki a garin Damietta, el-Sissi yace binciken hadarin ka iya daukan lokaci mai tsawo, yace amma da zara masu bincike sun sami amsoshin da suka gamsu dasu za'a sanarda jama'a.
Shi dai jirgin na Masar mai lamba MS804 ya tsunduma cikin tekun Barum ko Mediterranean ne a kan hanyarsa ta zuwa Alkahira daga Paris. Ya hallaka duka mutane 66 dake cikinsa. Masu bincike sun ce a daren Asabar aka ga hayaki yana fitowa daga cikinsa kafin jirgin ya fado. Naurar dake zaburar da jama'a idan akwai wani abun da bai kamata ba bata nuna wani dalilin hayakin ba.
Ministan zirga zirgan jiragen sama na kasar Sherif Fathy yace bisa alamu aikin ta'adanci ka iya zama sanadiyar gobarar ba wai matsalar da injin din jirgin ba.
Kawo yanzu dai babu wata kungiyar ta'adanci da ta dauki alhakin kai hari.