Ganin yadda yake babbar barazanar da rayuwar jama’a ke fuskanta a yankin Agadem inda kamfanin CNPC na kasar China ke ayyukan hakar man fetur ya sa Sarkin garin Lahari Mahamat Sanoussi tattaki zuwa birnin Yamai domin sanar da hukumomi halin da al’uma ke ciki kamar yadda ya bayyana a lokacin taron manema labarai na hadin guiwa da kungiyar ROTAB.
Sarki Mahamat Sanoussi cikin harshen tubanci ya ce suna cikin mawuyacin hali saboda haka wasu suka fara kaura domin kiwo shine aikin da suka fi dogaro akansa.
Ya kara da cewa, dabobinsu suna ta mutuwa basa samun sararin su yi kiwo saboda yadda ake ta jibge kayan aikin shimfida bututu. Ya ce Man fetur ba binda ya kawo masu sai matsaloli, ba makarantu, ba asibiti, ba ruwan sha kuma kamfanin China bai taba ba yaransu aiki ba.
Sarkin Lahari a zuwansa Yamai ya shigar da takardu a wasu ofisoshi da suka hada da ma’aikatar man fetur, Majalsar Dokoki, ofishi babban jami’i mai kula da shiga tsakani, amma shiru ba wata amsa mai gamsarwa.
Wannan ya sa shugaban kungiyar ROTAB mai fafitikar ganin an yi adalci a sh’anin ma’adanai Ali Idrissa jan hankulan mahukunta don a dubi wannan batu da idon rahama.
Sha’anin man fetur a Nijar wata harka ce da masu fafutuka ke gunaguni akai sakamakon rashin samun cikakken bayanii kan yadda ake gudanar da ita.
A shekarar 2011 Nijar ta fara sayar da man fetur da ake hakowa a kasar a kasuwa inda a kowace rana ake hako ganga 20000 daga rijiyoyin man Agadem dake yankin Diffa wadanda ake tacewa a matatar SORAZ dake Zinder.
Ganin yadda abubuwa ke tafiya kamar yadda ake bukata ya sa gwamnatin kasar hada guiwa da hukumomin jamhuriyar Benin don fitar da man zuwa kasuwannin duniya ta hanyar bututun da a yanzu ake gudanar da ayyukan shimfidawa.
Yunkurin jin ta bakin jami’ai a ma’aikatar man fetur dangane da irin wadanan korafe-korafe ya ci tura.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: