Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun bayyana cewa, sun yanke shawarar dage bukin FIMA karo na goma ne, bisa dalilan tsaro, biyo bayan harin ta’addancin da aka akai a makon jiya a birnin bamako na kasar mali da wadanda aka kai mako guda kafinsa a birnin paris na kasar faransa wadanda suka haddasa asarar rayukan mutane da dama .
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar tace ta dage wannan buki domin taya makwafta juyayin abinda ya samesu sannan tace matakin zai taimaka a kara karfafa kwanciyar hankali saboda haka tace wajibi ne jama’a su bada hadin kai.
Bakin da suka dako gari daga kasashen duniya daban daban domin halartar wannan buki na FIMA sun bayyana matukar kaduwa da jin sanarwar dage wannan haduwa ta kasa da kasa.
A gobe laraba 25 Nuwamba ya kamata a soma wannan buki sai dai a maimakon jawabin kaddamarwa gwamnatin Nijer ta hanyar kakakinta za ta sanarda jama’a matakin dage bukin a hukumance.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Sule Mumuni Bama ya aiko daga Nyamie.