A Turai, ministocin harkokin kudi na kasashe da suke cikin kungiyar sun amince a baiwa Girka dala miliyan dubu biyu da miliyan dari daya, a zaman wani bangare na yunkurin ceto kasar daga matsalolin tattalin arziki data shiga, bayan da hukumomi a Athens, suka zartas da wasu matakai na tilas da zummar yin garambawul ga tattalin arzikin kasar cikin makon jiya.
Jiya Litinin ne a hukumnce kungiyar ta EU ta amince da shirin, bayan da majalisar dokokin Girkan ta amince da sabbin matakai na tsuke bakin aljihu, da suka hada da karin kara kudin haraji,da haraji kan barasa, da kudin amfani da hanyoyi, da kuma takaita tallafin gwamnati da take baiwa wadanada suka gaza biyan kudin gidajen da suke ciki.