Shugaba Barack Obama ya dauki wannan matakin ne jiya Litinin ta wajen amfani da umarni ko dokar da ake kira "ta shugaban kasa."
Sun hada harda ministan tsaro Alain Bunyoni, mukaddashin darektan 'Yansanda Godefroid Bizimana, tsohon darektan hukumar leken asiri Godefroid Niyombare, da kuma tsohon ministan tsaro Cyrille Ndayirukiye.
Amurka tana zargin Bunyoni da Bizimana da laifin jagorancin masu cin zarafi da kuntatawa masu adawa da shugaba Pierre Nkurunziza. Ta kara da cewa Niyombare da Ndayirukiye sun taimakawa wajen haddasa rudani a Burundi lokacinda aka yi kokarin yiwa shugaban kasar juyin mulki cikin watan Mayu.
Umarnin da shugaba Obama ya bayar zaiyi daurin talala kan kadarorin mutanen nan hudu a duk inda Amurka take da iko. Kungiyar hada kan kasashen Turai EU da kungiyar hada kan kasashen Afirka AU suma sun aza takunkumi kan wadannan mutane hudu.
Ahalinda ake ciki kuma gwamnatin Burundi ta dakatar da kungiyoyin fara hula 10 wadanda suka nuna adawa da shirin shugaban kasar na yin tazarce.