Firayim Ministan Ingila David Cameroon jiya Litinin, yayi tayin tallafawa Faransa a ci gaba da farmakin da take kaiwa kan mayakan sakai na kungiyar Daesh ko ISIS a Syria. Yace zai nemi amincewar majalisar dokokin kasar wani lokaci cikin makon nan domin Britaniya ta shiga sahun yaki da masu ikirarin jihadin.
A lokacin wata ziyara da ya kai Paris, shugaban Ingilan ya gayawa shugaba Farncosi Hollande cewa jiragen yakin Fransa suna iya amfani da wani sansanin sojan sama na Ingila a Cyprus wajen kaddamar da hare hare kan muradun kungiyar Daesh ko ISIS, haka yace Ingila zata taimaka mata da jiragen sama masu dakon mai wadanda zasu iya durawa jiragen yakin Faransa mai a sararin samaniya.
A ci gaba da rangadi da kuma shawarwari na neman goyon baya da yake yi ahalin yanzu da wasu shugabannin kasashen duniya, yau Talata ake sa ran shugaba Hollande zai gana da shugaban Amurka Barack Obama. Daga bisani cikin makon nan zai je Moscow domin ganawa da shugaban Rasha Vladimir Putin.