Frayim Ministan Israila ya ce akwai yiwuwar kulla yarjejeniyar sulhu ta wucin gadi da Falasdinawa idan bangarorin biyu ba sa iya cimma jituwa akan manyan matsalolin da su ka yi shekaru suna warware tufkar da ake yi a fannin neman zaman lafiya, kamar maganar da ta shafi matsayin birnin Kudus da kuma ‘yancin Falasdinawa na iya komawa gida bayan sun jima da barin yankin su na asali.
A karon farko a jiya litinin, frayim minista Benjamin Netanyahu ya ambaci yiwuwar kulla wani fallen yarjejeniyar zaman lafiya, a cikin wata hirar da ya yi da wani talbijin din Israila mai suna Channel 10. Ya ambaci matsalolin da ake fuskanta game da matsayin birnin Kudus da kuma na ‘yan gudun hijira a zama abubuwa guda biyu mafiya tsaurin da ake gardama akan su wadanda kuma su ne su ka hana cimma cikakken zaman lafiya na dindindin.
Nan take babban mai tattaunawa da sunan Falasdinawa, Saeb Erekat ya yi watsi da ra’ayin na cewa ana iya yin wata yarjejeniya wai ta wucin gadi, ko kuma samar da wata mafitar da ba za ta warware dukkanin manyan matsalolin da ke raba kanun bangarorin biyu ba. Musamman ma ya fada cewa ba za a fasa yanke shawarar akan matsayin birnin Kudus da na Falasdinawa ‘yan gudun hijira ba.
Falasdinawa na neman kafa kasar su a yankin yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza, kuma gabashin birnin Kudus su ke so ya zaman mu su babban birnin kasar, sai dai Israila ta fi shekaru arba'in ta na mamaye da birnin wanda kuma ta ce shi ne babban birnin ta ar Mahadi Yabayyana,wanda kuma ba za a iya rabawa gida biyu ba.
Batutuwan birnin Kudus da kuma makomar dubban daruruwan Falasdinawan da su ka yi gudun hijira a zamanin yakin da aka yi a wajejen lokacin da aka kirkiri Israila a shekarar 1948, su ne matsalolin da ke hana cimma nasara a tattaunawar sulhun da aka yi shekara da shekaru ana yi.