Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu ta bada umurnin a ci gaba da tsare wasu mutane uku da aka kama a kasar Denmark bisa zargin shirin kai harin ta’addanci


Harin ta'addanci a Denmark
Harin ta'addanci a Denmark

Kotu ta bada umurnin a ci gaba da tsare wasu mutane uku da aka kama a kasar Denmark bisa zargin shirin kai harin ta’addanci

Kotu ta bada umurnin a ci gaba da tsare wasu mutane uku da aka kama a kasar Denmark bisa zargin shirin kai harin ta’addanci kan wata jarida ta Copenhagen, na tsawon makonni hudu dake tafe. Ana tsare da mutanen uku bisa tuhume-tuhume na kokarin aikata ta’addanci. Kotun ta saki mutum na hudu daga cikinsu a yau alhamis. Ana zargin mutanen dake tsaren, dan Tunisiya daya da ‘yan kasar Sweden biyu da laifin kulla makarkashiyar kai hari kan ofishin wata jarida ta birnin Copenhagen, wadda ta harzuka mutane da dama a kasashen Musulmi a bayan da ta buga wasu zane-zanen da ta ce na Annabi Muhammad (saw) ne. Hukumomi sun ce wadanda ake tuhumar sun yi niyyar kashe mutane masu yawa. Wani jami’in leken asiri ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa, an saki wani dan kasar Iraqi mai shekaru ashirin da shida da haihuwa mai neman mafaka a kasar, amma har yanzu ana bincikensa kan yana da hannu a makarkashiyar.

XS
SM
MD
LG