Papa Roma Benedict ya kira na a sami zaman lafiya a hudubarsa ta jajiberen kirsimeti, da ya gabatar cikin wani hali na karin matakan tsaro da aka dauka sakamakon harin bam biyu da aka kai a birnin Roma,ranar Alhamis.
Dubban jama’a ne suka halarci zaman ibadar da aka yi a cocin St,Peters Basilica dake birnin Vatican. Papa Roman ya yi addu’ar a sami zaman lafiya a wurare da ake fama fitinu a duk fadin Afrika kama daga yankin Darfur na Sudan,Ivory Coast,Somalia,da kuma yankin kwazazzabu.
An tsaurara matakan tsaro a cocin.Bara wata mace mai fama da tabin hankali duk da matakan tsaro, ta kutsa ta kada Paparoma.
Harin bam da aka kai ta aike su kamar wasika ranar Alahamis a ofisohin jakadanci biyu dake fadar kasar sun jikkata mutane biyu,dayansu raunukansu masu tsanani.
Wata kungiyar tsageru mai inkiyar FAI c eta dauki alhakin kai harin a ofisoshin jakadancin Chile da Swissland.
Wani jami’in ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar yace sai tay an auna harin kan wadan ofisoshin jakadancin ne saboda bada jumawan nan bane kasar Switzeland ta yankewa wani dan kungiyar hukuncin dauri,yayinda wani dan kungiyar kuma ya mutu a wani harin bam a Chile.