Bayan da ya kammala wata ganawa ta musamman da wakilan kungiyoyin dattawan arewacin Najeriya Mukaddashin shugaban Najeriya Farfasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatin kasar zata zare ido kuma ta dauki duk matakin da ya kamata domin tabbatar da ba'a bar mutane suna tayin maganganun da basu dace ba.
Farfasa Osinbajo yayi wannan tsokacin ne a daidai lokacin da yake cigaba da ganawa da shugabannin al'umman Najeriya daban daban. Ko yau ma ana kyautata zaton zai gana da shugabannin al'ummar Igbo. Bayan ganawa dasu zai gana da shugabannin Yoruba a kudu maso yammacin Najeriya.
Farfasa Ango Abdullahi na cikin dattawan arewan da suka gana da Mukaddashin Shugaban Najeriya Farfasa Osinbajo wanda yayi karin haske akan taronsu.
Yana mai cewa Mukaddashin Shugaban kasa ya nuna damuwa kwarai da gaske saboda abubuwan dake faruwa ba daidai ba ne dole a taru a san yadda za'a gyara.
Inji Farfasa Ango mutanen Igbo ne suka fara rigimar tun lokacin mulkin turawa. Yace sun kasa samun shugabancin kasa ta fuskar siyasa sai suka dauko bindigogi suna kashe mutane.Lamarin ya kaiga yaki inda aka cisu. Amma bayan yakin cikin shekaru hudu ko biyar aka nada daya daga cikinsu a matsayin mataimakin shugaban kasa lokacin mulkin Shagari wanda ma basu bashi kuri'u ko kashi biyar ba. Yace shugaban kasa na yanzu sau biyu yake dauko mataimakinsa daga cikinsu domin a jawosu a jiki. Ko a lokacin zaben da ya gabata sun ki dayansu ya zama mataimakin Shugaba Buhari.
Akan yadda za'a dakile kara aukuwar abun da Igbo su keyi, Farfasa Ango ya tambaya ko za'a yi yaki dasu ne? Yace kwana kwanan nan suka hana kowa fita a jihohinsu duk da cewa akwai mutane da dama da ba Igbo ba ne. Yace abun da suka yi tauyewa mutane hakkinsu ne saboda sun hana kowa fita. Ban da haka radiyo dinsu sai zagin mutanen arewa ya keyi. Yace shekaranjiya Uwazurike ya ziyarceshi amma Igbo suka kama zanginsa domin ya zo Zaria ya gana dashi. Suka ce shi ba shugabansu ba ne Kanu ne shugabansu yanzu.
Ga ahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.
Facebook Forum