Washington, dc —
Yau shirin ke bankwana da Malan Awwal Gurgu ko kuma Awal Mai masara dake N’gaoundere a Jamhuriyar Kamaru wanda asalinsa dan Najeriya ne da yawon duniya ya kai shi wannan kasa ta yankin Afrika ta tsakiya, inda da farko ya rungumi bara a matsayin sana’a kafin daga bisani ya koma gona don noman masara inda a karshen ya shiga sana’ar saye da sayar da masara abinda ya sa a yau ake kiransa Malan Awwal mai masara.
To a kashi na karshe na tantaunawarsu da wakilin Sashen Hausa Mouhamadou Rabiou bakon shirin ya yi bayani kan yanayin zamantakewa a tsakanin nakasassun Kamaru da al’ummar wannan kasa sannan ya kuma tabo batun ilimin masu bukata ta musamman.
Saurari cikakken shirin: