Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NAKASA BA KASAWA BA: Bayan Ayyukan Kere-kere Wani Mai Nakasa Ya Shiga Sana’ar Daukan Hotuna, Mayu 25, 2023


Souley Mummuni Barma
Souley Mummuni Barma

NIAMEY, NIGER - Shirin Nakasa Ba Kasawa ba na wannan makon ya karbi bakuncin Achirou Salissou Almou daya daga cikin masu bukata ta musamman dake fafutukar neman na kai a jihar Maradi dake Jamhuriyar Nijar.

A ci gaba da neman hanyoyin kare kansa daga harkar bara da wasu ke maida ita sana’a Achirou ya yi aikin kere-keren kayayyakin fata ya kuma yi aikin walda da kanikacin injinan adaidaita sahu, kafin daga bisani ya karkatar da harkokinsa kan sana’ar daukan hoto da yace ta fi shiga ransa a dukkan sana’oin da ya taba yi a baya.

Saurari cikakken shirin da Souley Moumouni Barma ya shirya ya kuma gabatar:

NAKASA BA KASAWA BA: Bayan Ayyukan Kare-kere Wani Mai Nakasa Ya Shiga Sana’ar Daukan Hotuna, Mayu 25, 2023  .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:01 0:00

XS
SM
MD
LG