Kungoyoyi masu zaman kansu da yawa daga jihohi talatin da shida na Najeriya ne suka taru a birnin tarayya Abuja a yayin da Majalisar Wakilai ta bude dandalin sauraren jawaban jama'a game da dokar sa ido akan ayyukan kungiyoyin. Kashi casi’in cikin dari na wadanda suka zo taron na sukar sabuwar dokar da Majalisar ke niyar yi.
Mr. Charles, mai aiki da cibiyar mata da matasa da raya karkara da ake kira NAWIKA a takaice, wanda ya fito daga jihar Nasarawa, yace idan gwamnati ta fito da wata doka karkashin wata hukumar da zata sa ido akan harkokinsu, kungiyoyin sun koma na gwamnati kenan ba masu zaman kansu ba.
Muhimmin abinda ya fi daukar hankali a tanade-tanade goma sha takwas da dokar zata kunsa, sun hada da sabunta rijistar kungiya duk bayan shekaru biyu, da cin tarar duk kungiyar da aka kama da wani laifi har ta naira dubu dari biyar.
Dan majalisar wakilan Najeriya, Ahmad Babba Kaita, ya bayyana cewa, ya kamata ace gwamnati ta sa ido akan kungiyoyin don tabbatar da suna bin ka’ida da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Ya kara da cewa, idan kungiyoyin na da wani korafi game da abin daya shafi gwamnati sai su sanarwa majalisa ita kuma zasu duba. Saboda wasu na amfani da irin wadannan kungiyoyin don yin abubuwan da ba su dace ba a kasa.
Mike Eboh na wata kungiya mai suna Health Care Coalition daga jihar Jigawa yace, wannan ba dalili bane, idan gwamnati na so ta kama kungiyoyin jabu da wadanda ke karbar kudade basa aiki, to su yi kokarin karfafa ma’aikatar tsare-tsare ta kasa. Ya kara da cewa kasashen da suka yi irin wadannan dokokin basu sami nasara ba.
Ga karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum