Nan ba da dadewa ba ‘yan kasashen waje irinsu China da sauransu za su rika ribibin zuwa arewacin Najeriya kafa jari saboda za a kafa wata makekiyar tashar makamashin gas a Ajakuta, inda za a shinfida bututai daga Ajakutan zuwa sassan arewacin Najeriya musamman ma Abuja da Kaduna da Kano. Sannu a hankali bututan za su isa wurare da dama na arewacin kasar.
Wannan tashar, wadda kafa ta zai ci dalar Amurka Miliyan dubu dari biyu ($200,000m) za ta magance matsalar rashin wutar lantarki a arewacin kasar ta yadda kamfanoni za su yi ta habaka. Yawan kamfanonin ciki da wajen Najeriya zai janyo ayyukan yi ga ‘yan arewacin Najeriya tare kuma da bunkasa tattalin arzikin yankin.
Kakakin Fadar Shugaban Najeriya Garba Shehu ya ce manyan kamfanoni su ma za su saka jari ciki ta yadda za a gudanar da tashar makamashin ba tare da cikakkiyar sa hannun gwamnati ba saboda a kula da tashar. Ya bayyana cewa muddun mutane su ka saka jari ciki to ba za su yadda a barnata wurin ba, Ya kwatanta irin kamfanonin da za a kafa sanadiyyar kafa tashar da irin kamfanonin da aka kafa a kuduncin Najeriya da kuma wasu kasashen Afirka, inda kasashe irin China da Turai ke ta saka jari saboda yalwar makamashin gudanar da manyan kamfanoni.
Ga Nasiru Elhikaya da cikakken rahoton:
Facebook Forum