Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya na daya daga cikin kasashe shida da aka fi mutuwa da zazzabin cizon sauro a duniya


Wadansu kanan yara dake fama da zazzabin malariya
Wadansu kanan yara dake fama da zazzabin malariya

Hukumar lafiya ta yi kiyasin cewa, kashi tamanin da biyar na masu mutuwa da zazzabin cizon sauro kananan yara ne.

Hukumar lafiya ta duniya ta yi kiyasin cewa mutane dubu shida da dari biyar ne suka mutu sakamakon kamuwa da zazzabin cizon sauro a shekara ta dubu biyu da goma, kashi tamanin da shida daga cikinsu kuma kananan yara da shekarunsu basu kai biyar ba.

A cikin rahoton shekara shekara da hukumar ta bayar a watan Disamba, Hukumar lafiya ta duniya ta yaba ci gaban da aka samu inda aka sami raguwar mutuwa sakamakon kamuwa da zazzabin cizon sauro da kashi ashirin da shida bisa dari.

Asusun yaki da zazzabin cizon sauro ya sami tallafin dala biliyan biyu bara ko da yake Hukumar lafiya tayi kiyasin cewa, za a bukaci kimanin dala biliyan biyar kowacce shekara har zuwa shekara ta dubu biyu da goma sha biyu idan ana son a cimma burin shawo kan cutar.

Kudin da aka samu ya taimaka wajen samar da gidajen sauro musamman a kasashen kudancin Sahara inda kimanin kashi hamsin bisa dari na mazauna yankin suka sami gidajen sauro idan aka kwatanta da kashi uku bisa dari da suka samu a shekara ta dubu biyu.

Darekta janar ta hukumar lafiya ta duniya Margaret Chan ta bayyana cewa, har yanzu rashin jin magani da zazzabin cizon sauro yake yi ya ci gaba da zama kalubala.

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa, zazzabin cizon sauro ya zama annoba a kasashe dari da shida yayinda ake yada cutar daga mutum zuwa mutum a kasashe casa’in da tara. Kashi sittin bisa dari na wadanda suke mutuwa sakamakon kamuwa da zazzabin cizon sauaro suna kasashe shida na duniya da suka hada da Najeriya da Damokaradiyar Jamhuriyar Kwango, da Burkina Faso da Mozambique da Ivory Coast da kuma Mali.

Aika Sharhinka

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG