Najeriya na daya daga cikin kasashe hudu da suka hada da Indiya da Pakistan da kuma Afghanistan da ciwon Inna yafi kamari a duniya. Sai dai rahoton da Hukumar Lafiya ta duniya ta bayar jiya na nuni da cewa, bisa ga ci gaban da aka samu a kasar Indiya, kasashen da cutar Polio tafi yaduwa zasu ragu zuwa uku, da suka hada da Najeriya da Afghanistan da kuma Pakistan.
Tsakanin shekara ta dubu biyu da tara zuwa dubu biyu da goma, an sami raguwar yaduwar ciwon inna da kashi 95%. Daga masu dauke da cutar dubu hudu da aka samu a shekara ta dubu biyu da uku, da kuma kananan yara dari shida da goma sha biyu da aka samu da cutar a shekara ta dubu biyu da takwas, zuwa yara ishirin da daya a shekara ta dubu biyu da goma.
Sai dai shirin yaki da cutar polio na duniya (Global Polio Eradication Initiave- GPEI) ya bada rahoto jiya cewa, an sami Karin wadanda suka kamu da cutar da kashi dari biyu da arba’in da takwas bisa dari a cikin shekara daya, inda aka sami yara hamsin da biyu dauke da cutar a Disambar bara ta dubu biyu da goma sha daya, daga ishirin da daya da aka samu a daidai wannan lokacin cikin shekara ta dubu biyu da goma.
A cikin rahoton GPEI na mako mako na nuni da cewa yajin aikin gama gari da ake yi a Najeriya da kuma hana zirga zirga a jihohi da dama ya shafi shirin rigakafi na kasa da ake shirin gudanarwa daga ranar hudu zuwa bakwai ga Fabrairu da kuma uku zuwa shida na watan Maris. An kuma janye zaman tattaunawa kan yadda za a aiwatar da shirin bisa wannan dalilin.
Sai dai an dauki ma’aikatan sa kai na al’umma domin aiwatar da shirin rigakafin a jihohin Kano, Kebbi da kuma Sokoto.