Darekta janar na cibiyar yaki da cutar kanjamau a Najeriya Farfesa John Idoko ya bayyana cewa, kimanin jarirai dubu saba’in ne ake haihuwa dauke da kwayar cutar HIV mai haddasa cutar kanjamau duk da ilimin fasaha da kwarewa da ake da ita ta jinya da kuma hana yada kwayar cutar HIV daga uwa zuwa jinjiri.
Farfesa Idoko ya bayyana haka ne a birnin Badun yayin wata bita da aka shirya kan kula da lafiyar mata masu juna biyu da kuma masu jego. Ya bayyana cewa, wannan ya zama babbar kalubala a ci gaban da aka samu a yunkurin rage yaduwar cutar kanjamau a Najeriya.
Bisa ga cewar Farfesa Idoko, jinyar mata dake dauke da cutar kanjamau hanya ce muhimmiya ta hana yada kwayar cutar HIV, sabili da haka akwai bukatar ba mata masu juna biyu da suke dauke da kwayar cutar maganin rage kaifin cutar da ake kira ARV.
Shugaban hukumar yaki da cutar kanjamau na Najeriyan ya bayyana takaicin ganin gibin da ke akwai da cewa, adadin sababbin wadanda suke kamuwa da cutar ya haura jinyar a ake yi, sabili da haka Najeriya tana bukatar cuta yaki da cutar kanjamau a cikin wadansu ayyukan jinyarta kamar yaki da tarin fuka da zazzabin cizon sauro domin ganin maganin kashe kaifin kwayar cutar HIV ya isa kowanne sako, a kuma tabbata mutane suna samun magani da zarar an gane suna dauke da kwayar cutar.
Bisa ga cewar Farfesa Idoko, kashi 70% na ‘yan Najeriya suna zaune ne a yankunan karkara sabili da haka amfani da tsarin kiwon lafiya matakin farko ita ce hanya mafi sauki ta yaki da cutar kanjamau a karkara.
Shugaban yaki da cutar kanjamau a Najeriya ya bayyana cewa, matasa da dama basu da cikakken ilimi game da cutar kanjamau. Bisa ga cewarshi, kimanin kashi 60% na al’ummar Najeriya basu san ko suna dauke da kwayar cutar HIV ba ko kuwa babu. Yayinda wariya da kyamar da ake nunawa masu dauke da kwayar cutar yake hana da dama zuwa su yi gwaji domin sanin ko suna dauke da kwayar cutar.
Ya kuma bayyana kalubalan da ake fuskanta a yaki da cutar kanjamau da suka hada da karancin kudi, da halin ko in kula da ‘yan siyasa ke nunawa a yaki da cutar a matakin jiha da kananan hukumoni hadi da karancin kudi da wadannan matakan gwamnatin ke fuskanta. Sauran matsalolin kuma sune rashin ingancin jinyar mata masu ciki dake dauke da kwayar cutar yadda jaririn da zasu Haifa ba zai dauka ba,, da rashin isassun jami’an aiki da cibiyoyin jinyar da za a iya kula da mata masu juna biyu da ke dauke da cutar kanjamu da kuma banbancin jinsi da talauci duka sun hadu sun sa cutar tana neman ta zama annoba.