Bayan tonon sililin da ya bayyana na cewar akwai yiwuwar Shugaban Kasa Trump ya bukaci tsohon shugaban hukumar FBI James Comey da ya yayi watsi da binciken da ake yiwa tsohon mai ba shugaba Trump shawara kan harkokin tsaron kasa Micheal Flynn, wani jigon dan jam’iyyar Republican mai jagorancin wani kwamitin majalisar dokoki ya bukaci hukumar FBI da ta bada rubutaccen bayanin Comey da abinda ya faru cikin wannan makon.
A wasikar da ya rubutawa mai rikon kujerar shugaban hukumar ta FBI Andrew McCabe, Shugaban Kwamitin sanya ido akan ayyukan gwamnati na majalisar wakilan tarayya, Jason Chaffetz, dan jam’iyyar Republican ya bukaci Duk wani abu da ya shafi takaitaccen bayani, Sauti da aka dauka ko kuma wani sako da ya shiga tsakanin Comey da Shugaban Kasa da a bayyana shi ga Kwamitin kafin ranar 24 ga watan Mayu.
Jaridar New York Times ita ta fara fallasa wannan labarin a daren jiya Talata, inda ta bada rahoton Comey ya rubuta cikakken bayanin tattaunawar sa da shugaban kasa bayan Flynn ya sauka daga kan mukamin sa a watan Fabrairun da ya gabata. Labarin na jaridar New York Times ya ce rubutun na daya daga cikin shaidu na takarda da Comey ya bari domin nuna cewar bukatar ta Shugaban kasa ba a bisa ka’ida aka yi ta ba.
Masu sharhi akan harkokin shari’a da dama sun ce irin wannan bukatar ta shugaban kasa ka iya kasancewa hana ruwa gudu a fannin shari’a, Laifin da ka iya sawa a tsige shugaban.
Facebook Forum