Shugaban masu rinjaye a majalisar Dattawan Amurka, Mitch McConnell, na fuskantar turjiya kan shirinsa na ganin an kada kuri’a, domin yin watsi da tsarin kiwon lafiyan kasar, bayan da yunkurin baya-bayan nan kan yin garambawul ga fannin tsarin kiwo lafiyar kasar ya cutura a farkon makon nan.
McConnel ya bayyana sabuwar hanyar da za su fuskanci shirin kiwon lafiya a jiya Talata, yayin bude majalisar, inda ya ce za su bullo ta wata fuska “domin samarwa Amurkawa sauki daga shirin Obamcare” kamar yadda ake wa tsarin kiwon lafiyar inkiya hade da sunan tsohon shugaba Barack Obama.
Sanatoci daga bangaren Republicans da suka hada da Shelly Moore Capito da Susan Collins da kuma Lisa Murkowski, sun bayyana cewa ba za su goyi bayan shirin na McConnell ba, yayin da Rob Portman da wasu sanatocin suka nuna shakkunsu kan shirin sauya tsarin kiwon lafiyan na Obamacare.
Wannan alamun shan kasa da kudurin yake fuskanta, shi ne na biyu cikin watanni da dama, wanda hakan cikas ne ga shugaban masu rinjaye McConnell, wanda a watan Yuni, sai dai ya soke wani shirin kada kuri’a da ya lura da ba su da cikakken goyon baya.
Shugaban Amurka Donald Trump wanda ya jima yana neman a kawar da tsarin na Obamacare, ya ce ya ji matukar takaici da yunkuri sauya tsarin kiwon lafiyan na Obamacare ya fuskanci cikas.
Su dai ‘yan Republican su ke da rinjayen sanatoci 52 a majalisar dattawan kasar yayin da ‘yan Democrat ke da 48, adadin da ya bar dan karamin gibi tsakanin bangarorin biyu da kuma yake bai wa ‘yan Democrat din damar yin tutsu ga duk wani kuduri da bai yi masu ba, musamman idan suka samu goyon bayan wasu daga 'yan Republican.
Facebook Forum