Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Shugaban Amurka Zai Gurfana Gaban 'Yan Majalisar Kasar


Da alamu 'dan shugaban Amurka da sirikinsa Jared Kushner, zasu gurfana gaban kwamitin tattara bayanan sirri na Majalisar Dattawan Amurka.

Jigogin ‘yan Majalisun Amurka masu bincike kan katsalandan ‘din kasar Rasha a zaben shugaban ‘kasa na shekarar 2016, na bukatar ‘dan shugaba Donald Trump na farko ya gurfana gabansu domin bada bahasi kan ganawar da yayi cikin watan Yuni da wata lauyar Rasha, da ake akayi tunanin tana da bayanai da zasu iya bata mutuncin abokiyar takarar mahaifinsa Hillary Clinton.

A jiya Alhamis ne shugabar marasa rinjaye a Majalisar Dattawa Nancy Pelosi, ta rubuta a shafin Twitter cewa “Bayanin da aka bada cewa kwamitin kamfen ‘din shugaban kasa Donald Trump yayi kokarin hada kai da Rasha, wani abin takaici ne.”

Ko bayan babban ‘dan Donald Trump, shima sirikinsa Jared Kushner ana kyautata tsammanin zai gurfana gaban Majalisa. Haka kuma ‘yan Majalisu na jam’iyyar Democrat na bukatar a janye izinin tantancewar tsaro ta Kushner da kuma babban mai baiwa shugaban shawara.

Su kansu ‘yan Majalisun jam’iyyar Republican sun fadi cewa zai kasance abin alkhairi ga shugaban kasa ya janye ‘ya ‘yansa daga harkokin gwamnati, ciki harda Kushner wanda ke auren ‘yar shugaba Trump ta farko, Ivanka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG