Kasar Afurka ta Kudu ta fara tantance barnar da tashin hankalin kin jinin bakin haure na wannan mako ya janyo, wanda a cewar hukumomi rikicin ya hallaka mutane goma kana wasu da dama sun jikata, ya kuma jefa kasar cikin tsoro da tabarbarewar harkokin kasuwanci haka zalika ya kuma yi illa ga dangantakar kasar da wasu kasashen Afrika.
A wani jawabi da ya yi ta telbiji a jiya Alhamis, shugaba Cyril Ramaphosa, ya yi Allah wadai da hare haren da aka fara a ranar Lahadi, wanda masu manyan motoci da masu tunanin bakin haure sun kwace musu ayyuka a kasarsu su ka shirya.
Sai dai an kai hari a kan daidaikun mutane kana an lalata gidaje da wuraren kasuwanci.
Ramaphosa ya ce mutane biyu daga mutane goma da suka mutu ‘yan kasar waje ne, koda yake bai fadi kasarsu ba.
Ya kuma ce an kama mutane 423 a lardin Gauteng da ke arewa maso gabashin kasar, yankin da Johannesburg da babban birnin kasar Pretoria suke.
Facebook Forum