Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kwatanta rasuwar babban hafsan sojojin kasa Laftanar Janar Ibrahim Attahiru a matsayin wani abu da zai haifar da koma baya ga kasar.
Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar a ranar Juma’a sa’o’i bayan rasuwarsa.
Janar Ibrahim Attahiru ya rasu ne a wani hatsarin jirgi da ya auku a kusa da filin tashin jirage da ke Kaduna a arewa maso yammacin kasar.
Jirgin ya taso ne daga Abuja zuwa Kaduna a cewar wata sanarwa da rundunar sojin Najeriyar ta fitar.
“Hadarin jirgin, ya yi mana kwaf daya a makasa, a kuma daidai lokacin da dakarunmu suka samo bakin zaren kawo karshen matsalar rashin tsaro da kasar ke fuskanta.” Muhammadu Buhari ya ce a sanarwa ta Shehu wacce ya wallafa a shafin Twitter.
Buhari wanda ya yi addu’a ga mamatan, ya sha alwashin ba za a manta da irin saudakarwar da suka yi ba.
Karin bayani akan: Janar Ibrahim Attahiru, Boko Haram, sojoji, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
A daren ranar Juma'a ministan tsaron kasa Janar Bashir Salihi Magashi (rtd) ya je fadar Buhari ya yi masa karin bayanin kan hatsarin.
A watan Janairu, Buhari ya nada Janar Ibrahim Attahiru, wanda ya gaji Janar Tukur Buratai tare da sauran hafsoshin sojojin kasar.
Wannan shi ne karo na uku a wannan shekara da jirgin sojin Najeriya ke yin hatsari ko ya bata a neme shi a rasa.
A halin da ake ciki fadar shugaban kasar, ta fitar da sunayen mutum 11 da suka mutu a hatsarin jirgin:
- Lt Gen. I. Attahiru
- Brig Gen. MI Abdulkadir
- Brig Gen. Olayinka
- Maj. LA Hayat
- Maj. Hamza
- SGT Umar
Matuka Jirgin Da Masu Hidima
- FLT LT TO Asaniyi
- FLT LT AA Olufade
- ACM Oyedepo