Hukumar yara ta MDD tace idan ba a kai daukin gaggawa ba yara Dubu 75 ne zasu iya rasa rayukansu zuwa shekara mai zuwa, inda yara Dubu 400 zasu bukaci tallafin gaggawa don rashin abinci don rashin abinci mai gina jiki da suke fuskanta.
Gwamnatin Najeriya da jihohin yankin na tura kayan abinci ga sansanonin gudun hijira, wanda kuma hakan baya wadata saboda yawan masu bukatar tallafin.
A cewar tsohuwar babbar jami’ar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Najeriya, Hadiza Sani Kan Giwa, hukumomin gwamnatin tarayya suna yin iya bakin kokarinsu ganin cewa an shawo kan al’amarin, haka kuma gwamnain tarayya ta kafa kwamitoci masu yawa da zasu gano hanyar da za a bi don tunkarar lamarin kasancewar yawan ‘yan gudun hijirar da ake da su.
Kwato garuruwa daga hannun ‘yan Boko Haram yasa aka gano yawan mutane manya da kanana dake fama da karancin abinci. Haka kuma fara samun kwaciyar hankali yasa aka fara noma a wasu sassan yankin da bullowar kalubalen yadda wasu ‘yan baranda ke saye abincin suna boyewa domin abincin yayi tsada su fitar suci karamar riba.
Domin karin bayani.