Kodayake fashewar nakiyar bata raunatashi ba amma yayinda ya sauko daga motarsa ya duba irin illar da nakiyar tayi nan take mayakan Boko Haram dake boye suka bude masa wuta lamarin da yayi sanadiyar mutuwarsa da jikata wasu sojojin dake tare dashi.
Kanar Aminu Isa Kontagora tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kano yace abun da ya faru alama ce dake nuni cewa akwai matsala. Yace yakin sunkuru yana da wahala. Tunda aka hana 'yan Boko Haram kama garuruwa yanzu harin sari ka noke zasu dinga kaiwa sojoji. Idan sojojin suka dinga lura zasu iya magance matsalar.
Shi ma kwararre kan sha'anin tsaro Dr. Bawa Abdullahi Wase ya bukaci rundunar sojojin Najeriya da ta yi binciken kwakwaf kan sojojinta dake yaki a arewa maso gabas. Inji shi 'yan Boko Haram dake barna yanzu wadanda suke cikin jami'an tsaron ne. Yace tun farko ya fada kuma zai sake fada idan ba tankade da rairaya aka yi ba to ire-irensu zasu cigaba da yin barna. Yace matakin farko da yakamata a dauka shi ne a cire duk sojojin dake yankin yanzu a kawo sabbi. Idan ko ba'a yi hakan ba to ba'a gama jin barna ba, inji Dr Wase.
Dr. Abubakar Mu'azu na jami'ar Maiduguri yace abun da ya faru abun bakin ciki ne. Yace bayan nasarorin da sojojin suka samu a ce an kai wani matsayi inda yau ana kashe masu kwamandoji ba kamara hasara kasar tayi ba. Yayi imani akwai wasu cikin sojojin da suke baiwa Boko Haram bayanan siri. Yace wajibi ne rundunar sojojin ta tashi tsaye ta zakulo munafukan dake cikinsu.
Shi ma Dr. Abubakar Umar Kari na jami'ar Abuja yayi gargadin cewa har yanzu Boko Haram na nan da karfinta duk da ikirarin da sojojin Najeriya keyi na cewa sun fi karfinsu.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.