A Iraqi, mutane dubu 30 ne suka fita daga birnin Fallujah cikin kwanaki uku da suka wuce, yayinda sojojin Iraqi suka kutsa tsakiyar birnin suka tilastawa mayakan sakai na ISIS zuwa arewa maso yammacin birnin.
Duk da dan karen zafin bazara a kasar, wasu mutane masu yawa wadanda suka tsere, a fili haka suke kwanciya ganin sansanonin 'yan gudun hijira sun cika makil. Wasu sun sami mafaka masallatai ko kuma a gine-ginen da ake adana kaya.
Ana kiyasin samada mutane dubu sittin ne suka sami gudu daga birnin.
Kungiyar agaji mai kula da 'yan gudun hijira daga kasar Norway, wacce take samar da abinci da ruwan sha na kwalba ga dubban mutanen, tace yawan mutane da kuma rashin tsari, ya hana su kaiwa ga ga dukkan sababbin 'yan gudun hijirar da suka isa inda suke.