Ambaliyar ruwa da zaizaiyar kasa a Indonesia sun kashe akalla mutane 35, yayinda wasu 25 kuma har yanzu ba'a san inda suke ba. Lamarin ya auku ne a tsakiyar birnin Java.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi, ya shafi dubban gidaje, wasu masu yawa suna cikin ruwa.
Masu aikin ceto suna neman wadanda ya-Allah suna nan da rai a Java, dake can ta kudancin kasar, wanda shine tsibiri mafi girma, kuma inda babban birnin kasar Jakarta yake.
Ambaliya ruwan da gocewar laka ba sabon abu bane a Indonesia, wacce take fuskantar irin wadannan bala'o'i, kasa ce da ke da jama'a sama da milyan 250. Java ne tsibiri mafi yawan jama'a a duk fadin duniya.