Garuruwan biyu wanda dubban mutane ke zaune a cikin su, suna kewaye ne cikin tsaunuka kuma babu hanya da kowanne irin abin hawa zai iya bi. A cewar Jonathan Jibril, wanda ke zama shugaban matasan garuruwan yace, suna fama da macizai ta ko ina saboda duk gonaki da ma kan duwatsu babu inda babu su. Kuma suna cizon mutane har a gidajen su.
Wani abin tada hankali shine yadda ake samun mace macen mata da yara wajen haihuwa, inda matan da suke mutuwa sukafi wanda suke haihuwa yawa. Hajiya Sa’adatu Mustapha Sa’ad Alkyabban Kaltingo, tace matsalar rashin hanyoyin da ake fama da su na daga cikin adilan da suka saka ake rasa rayukan wasu mata.
Bisa halin damuwa da mutanen yankin ke ciki kan wannan lamari yasa mai martaba Sarkin Kaltingo, Injiniya Sale Mohammed, hada gangami domin yin aikin gayya domin samar da hanya da akalla babur ko mota zasu iya bi domin dauko marasa lafiya a kaisu Asibiti cikin sauki.
Domin karin bayani.