Hukumomin tsaro a jihar imo sun yi Karin bayani kan wani mummunan hari da wasu yan bindiga da ake zargin 'yan rajin kafa kasar Biyafra ne suka kai kan hedikwatar Hukumar Zabe ta Jihar Imo, da ke yankin na kudu maso gabashin kasar.
A wannan hari dai an tabbatar da salwantar rayuka a kalla biya, baya ga asarar dinbin dukiyoyi.
Wannan harin dai, bayanai sun tambatar da cewar an Kai shi ne ta hanyar jefa abubuwa masu fashewa, in da aka tabbatar cewa maharan sun kona Sashen Tattara Bayanai na hukumar, haka kuma an halaka mutane da dama. Rundunar 'Yan sandan jihar ta Imo ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta ce akalla mutane biyar ne suka halaka, daga ciki kuwa akwai Jami'anta guda biyu , haka kuma rundunar ta samu nasarar halaka 'yan bindiga ukku tare da kwace bindigogi shida kirar Ak 47 .
Muhammad Barde shine Kwamiahinan 'Yan Sandan jihar ta Imo kuma ya yi karin haske kan abin da ya faru da kuma matakan tsaro da ake kara daukawa, kamar yadda za a ji idan an dangwali abin sauti.
Shi ma wani ganau ya ce wasu 'yan bindiga ne dauke da makamai su ka kai hari kan ofishin hukumar zabe ta jihar Imo, da misalin karfe uku saura kwata na safiyar yau; kuma sun hallaka mutane da dama.
Wakilin Sashen Hausa ya ga gawarwakin 'yan sanda guda biyu.
Yayin hare haren, 'yan bindigar sun kada wasu abubuwa masu fashewa sun kona wasu motoci baya ga yin kaca kaca da cikin ginin hedikwatar hukumar zaben. Daga bisani dai jami'an tsaro sun kai dauki amma dai kawo yanzu zaman dardar a jihar ta Imo ake yi.
'Yan bindigar IPOB dai masu rajin kafa kasar Biafara a yankin na kudu maso gabashin Najeriya, ko a baya can ma sun ce sun lashi takobin ganin cewa ba a gudanar da zabe a yankin nasu ba. Sun shiga kai hare hare kan ofisoshin hukumar zabe ta kasa a sassan yankin.
A halin da ake ciki kuma, Rundunar 'Yan Sandan jihar Ebonyi ta ce labudda za a gudanar da zabe a jihar ta Ebonyi, duk da turjiyar 'yan bindigar. Aliyu Garba Kwamiahinan Yan Sandan jihar, shi da kansa ya tabbatar da hakan, kamar yadda za a ji idan an dangwali abin sauti.
Saurari cikakken rahoton Lamido Abubakar: