A Najeriya, yayin da ake shirye-shiryen babban zabe a shekarar 2023, hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta INEC ta ce akwai dubban katunan da aka yi wa rijista da masu su basu karba ba, duk da cewa wasu sun koka kan cewa ba a basu katunansu ba.
Hukumar ta bayyana cewa akwai jimlar katunan zabe 229,583 da ba a karba ba a jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara, adadin da ke iya yin babban tasiri wajen zaben shugaba na gari.
Shugaban sashen kula da fasahar sadarwa ta zamani na hukumar Abubakar Usman, yace katunan sun hada da na baya da ba a karba ba a zaben 2019 da wadanda aka yi wa gyara ko canjin wuraren jefa kuri'a.
A jihar Kebbi, hukumar ta ce akwai katuna 63,717 da ba a karba ba inda kakakin hukumar Atiku Shekare ya ce masu zuwa neman su yanzu, wadanda suka yi rijista ne daga baya.
Hakazalika a jihar Zamfara, jami'in sadarwa da wayar da kan jama'a na hukumar zabe Ibrahim Bello, yace akwai dubban katuna da ba a karba ba da yawan su ya kai 39,873 kuma an kai su mazabu an rarraba, yanzu hukumar na kan kokarin sauke lambobin waya na masu katunan don a sanar da su.
Duk da haka masu jefa kuri'a da yawa sun koka kan cewa basu da katunan zabe da aka yi wa rijista, ko da yake kakakin hukumar zaben jihar Kebbi Atiku Shekare, yace masu wannan korafin in dai ba masu sabuwar rijista ba ne, watakila irin mutanen nan ne da ke jira a kawo musu katin su a runfunan zabe.
Saurari rahoton cikin sauti: