ABUJA, NIGERIA - Sai dai hukumar ta ba da tabbaci kan inganci da tsaro da ke tattare da yin amfani da na’urar B-VAS tare da cewa ba za’a iya misalta tasirin na’urar da na baya da ake sanya katin zabe a ciki ba wanda aka yi amfani da shi a zabukan da suka gabata na shekarar 2011 da 2015 ba.
Hukumar Zaben ta INEC dai ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ba za a iya yi wa tsarin tantance masu kada kuri’a na Bimodal BVAS zagon kasa ba, saboda an tsare shi kuma ba za a iya kai kutse cikinta ba, kamar yadda Zainab Aminu Abubakar jami’a a sashen yada labarai a hukumar ta bayyana mana.
A yayin da wasu yan’ Najeriya ke nuna fargaba a game da tasirin wannan na’ura ta BVAS a yankunan da babu wutar lantarki balle tsarin INTERNET wadanda ake amfani da su wajen tafiyar da na’urar, kwarare kan sha’anin tsaron yanar gizo ya yi karin haske kan yadda na’urar ke aiki.
A wani bangare kuwa masani kuma mai sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya Dakta Faruk BB faruk cewa ya yi idan ana sara ana duba bakin gatari saboda ana iya samun tsaiko ko tangarda a yayin amfani da na’ura irin ta bature.
Duk da shakkun da al’umma Najeriya ke da shi game da tasirin nau’rar BVAS wajen gudanar da babban zaben shekarar 2023 da ke tafe, hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta yi alkawarin tabbatar da kare kuri’un ‘ƴan kasar tare da kari kan cewa zamanin magudin zaɓe ya wuce.
Saurari cikakken rahoto daga Shamsiyya Hamza Ibrahim: