Wata mummunar musayar wuta da wasu sojoji da ‘yan sanda suka yi a Birnin Aba na jihar Abia ranar Juma’ar da ta gabata ta yi sanadiyar mutuwar ‘yan sanda biyu da soja daya tare da raunata mutane da dama.
Gwamnatin jihar Abia ta sake jaddada aniyarta na daukan mahimman matakan shawo kan dambarwar tare da tabbatar cewa ba’a sake samun irin hakan ba a jihar.
Kwamishanan yada labaran jihar Chief John Okiyikalu ya sanar cewa da jin aukuwar lamarin gwamnatin jihar ta yi maza maza ta taro shugabannin sojoji da ‘yan sanda domin ganawar gaggawa da zummar yayyafawa rikicin ruwan sanyi. Gwamnatin ta kuma kai dokin gaggawa domin ceto rayuka.
Bugu da kari gwamnan jihar Abia ya kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin rikicin tare da sanin matakin da za’a dauka na hana sake aukuwar lamarin. Jihar tana son ta tabbatar jami’an tsaron suna aiki tare cikin kwanciyar hankali da lumana.
Hukumomin ‘yan sanda da sojoji sun ki su ce komi akan abun da ya faru.
Sai dai wani tsohon soja mai ritaya dake sharhi akan harkokin tsaro ya yi tsokaci yana mai cewa “Sojoji suna da nasu aikin da tsarin mulki ya tsara masu, na kare mutuncin kasa yayinda aikin ‘yan sanda ne su inganta matakan tsaron cikin gida. Amma idan aka hada sojoji da ‘yan sanda su yi aiki tare dole a samu matsala saboda haka wajibi ne gwamnati da dinga waresu”.
Tsohon sojan yace bai kamata ana tura sojoji su yi aikin da ‘yan sanda ke yi ba.
Alphonsus Okoroigwe nada karin bayani a wannan rahotonsa
Facebook Forum