Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Matsalar 'Yan Bindiga A Najeriya Ya Ki Ci Ya Ki Cinyewa


Wani dan tawaye
Wani dan tawaye

Matsalar yan bindiga a bangarorin Najeriya daban-daban, wani babban al'amari ne da ke barazana ga sha'anin tsaro a Najeriya idan aka yi la’akkari da yadda matsalar ke kara kazancewa musamman a jihohin da ke Arewa maso Yamma da Tsakiya.

Al'amarin dai da ya faro daga aika-aikar barayin shanu a wasu sassan jihar Zamfara da makwabciyarta jihar Kaduna, sannu a hankali ya rikide zuwa rikicin manoma da makiyaya wanda a yanzu kuma ya juye zuwa kashen-kashe na ‘yan bindiga. Abin da masana tsaro ke cewa na da tada hankali.

Kananan hukumomin Anka, Maru, Birnin Magaji da ma wasu yankuna a jihar Zamfara da Birnin Gwari a Jihar Kaduna, da kuma Yankin Alawa a Jihar Niger, a kusan kullum sai an samu rohoton kashe-kashe na ‘yan bindiga.

Al'amarin ya fantsama zuwa jihohin Benue, da Taraba, da Nasarawa, da Kogi da Adamawa inda rigingimun ke daukar wani sabon salo da a lokuta da dama ke zama na makiyaya da manoma, da kabilanci ko ma na addini.

A baya dai abin ya kai sai da rundunar sojojin kasar ta kaddamar da wani Atisayen Tseren- Mage da tai mai lakabi da Operation Ayem Akpatuma a jihohin da ke tsakiyar Najeriya; da Operatiion Sharan Daji a jihohin Kaduna da kuma Zamfara, da Operation Karamin Goro a jihar Neja.

Ko a watan jiya ma, sai da hedikwatar sojin Najeriya ta fara atusayen Idon Raini a Birnin Gwari, bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a kafa wata bataliyar aiki da cikawa a Birnin Gwari.

A cewar wani masanin tsaro, Salihu Othman Dantata, da mamaki a ce dakarun sun gaza shawo kan wannan matsalar tsaron duk da dimbin kudaden da ake kebewa don aikace-aikacen jami'an tsaro a yankunan.

Ko nawa ne ake warewa duk wani atusayen sojoji da ake kira Operation? Tambayar kenan da wani jami'in tsaron da bai son a ambaci sunansa ya yi kenan.

Tsohon jami'i a hedikwatar leken asirin sojin Najeriya, Aliko Elrashid ya bayyana cewa idan ana son kawo karshen wannan matsalar tsaro, to dole ne gwamnatin ta dauka cewa wannan wani babbar matsala ce da ya kamata a maida hankali sosai. Sannan a shigo da rundunar sojojin saman kasar cikin atusayen domin kai hare-hare ta sama.

Ya ce muddin aka yi haka to ba makawa za a shawo kan matsalar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG