A kokarin shawo kan yawaitar rikicin dake faruwa a jihar Kaduna, sabuwar hukumar samar da zaman lafiya ta ce ta yi wani tsari na shekara biyar da zai kaiga samun zaman lafiya.
Malam Sale Umale daya daga cikin kwamishanonin hukumar samar da zaman lafiyar ya yiwa manema labaru karin bayani jim kadan bayan da suka kammala wani ataro akan yadda za’a shawo kan matsalar da ta addabi jihar.
Yace ana taro ne da jami’an tsaro da kafofin yada labarai wadanda suka aiki a jihar Kaduna. Suna nazarin abubuwan da ya kamata a yiwa matasa ta yadda za’a sauya tunanensu da ayyukansu daga son tada hankali zuwa ayyukan samun zaman lafiya.
Sale Umale, yace tsarin ya kuma tanadi yadda malamai masu karantarwa a makarantu zasu bada kyakyawar tarbiya domin samun zaman lafiya. Su kuma iyaye su fahimci mahimmancin samun zaman lafiya da irin tarbiyar da ya kamata su yiwa ‘ya’ya a gida.
Su ma sarakuna, tsarin zai jaddada yadda zasu warware sabani a cikin al’umma da ba zai hadasa tashin hankali ba. Hatta ‘yan siyasa tsarin zai ko kuma ya tanadi ka’idodin da ya kamata su yi anfani da su ta yadda duk lokacin da suke yakin neman zabe su sanya sakonin samun zaman lafiya cikin kalamunsu. Malam Sale sai yace wadannan su ne abubuwan da suke son su yi nan da shekaru biyar domin su sauya tunane zuwa ga tafarkin zaman lafiya.
Abdulaziz Ahmed Kadir wanda yake aiki da gidan rediyo da talibijan na Liberty y ace dan jarida ya san sai an samu zaman lafiya ne zai iya tashi ya yi aikinsa. Dan jarida ya san sau tari dan siyasa yak an yi magana ne akan abun da zai anfaneshi ba kasar gaba daya ba.
Ita ko Mawu Sheyi dake aiki da Freedom Radio dake Kaduna, ta ce sun koyi abubuwa da dama. Ana kokarin a ga yadda za’a fito da hanyar samun zaman lafiya. Ta ce su ‘yan jarida suna da aiki sosai ganin cewa duk rahoton da zasu dauka ya kasance na kawo zaman lafiya ne ba harzuka tashin hankali ba.
Isah Lawal Ikara nada karin bayani a rahotonsa
Facebook Forum