Yau dai ‘yan matan makarantar Chibok tamanin da biyu (82) da ‘yan kungiyar Boko haram suka yi musanyarsu da wadansu mayakan ta suka gana da iyayensu a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, inda suka ta kukan murna saduwa da iyayensu, a karon farko tun bayan sako su.
Bayan wannan kukan murna sai wurin ya kaure da rawa da wake wake iyayen suna cike da farin ciki suna ta rugume ‘ya’yan nasu.
Shugaban ‘yan assalin Chibok, wanda ya jagoranci iyayen daga garin Chibok, Yakubu Inkeke, ya nuna farin cikinsa tare da na alumar Chibok duk.
Ya ce a zamansa na shugaba yana gani cewa har yanzo ‘yar sa ta assali bata fit aba tukunna domin dukkan ‘yan matan ‘ya’yansa ne saboda haka idan dukkansu ba a sako su ba tofa murnarsa takaitaciyace.
Ya kuma kara da cewa yana godiya ga jami’an tsaro da suke sayarda ransu suna shiga daji domin ceto jama’an da ‘yan Boko Haram suka sace abun farin ciki ne, kuma a cewarsa suna da ban gaskiya cewa gwamnatin Najeriya, sata ceto sauran ‘yan matan.
A halin yanzu dai kungiyar rajin kwato ‘yan matan Chibok, watau BBOG tace tana fata gwamnati zata ci gaba da kokarin kwato sauran ‘yan matan dari da goma sha uku da har yanzu suke hannun ‘yan Boko Haram.
Facebook Forum