Horon da matasan suka samu zai basu damar iya sana'o'i ko aiki ta hanyar yanar gizo da kuma samun dabarun yaki da zaman kashe wando.
Wasu cikin wadanda suka samu horon sun bayyana yada suke ji a zukatansu.
Caleb Ibrahim daga karamar hukumar Kurmi ta jihar Taraba yace ya ji dadi domin idanusa sun bude saboda haka ba zai sake zama a gida ba yana kukan rashin samun aiki.
Inji Caleb zai iya samun abun yi har ma ya biya ma kansa bukata. Shi ma Abullahi Shuaibu yace horon nada matukar anfani sosai. Yace duk wanda yayi karatu daga Sakandare zuwa sama ya samu abun yi.
Shi ko Natafar Dogo yace yanzu ya samu ilimin da zai yi aiki da kwamfuta. Ya yiwa shugaban kasa Muhammad Buhari wanda ya kirkiro da shirin godiya
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Facebook Forum