A jihar Bauchi Center for Juvenile Delinquency Awarenes ko kuma cibiyar waye kawunan al'umma akan tabarbarewar tarbiyar yara, ita ce ta shirya gangamikan batun yaki da cin hanci da rashawa.
Shugabar cibiyar Hajiya Halima Baba Ahmed tace cin hanci ya samo asali ne tun daga cikin gidaje. A da babba na iya aikan yaron anguwa koina. Idan yaro ya ga babba da kaya ma zai karba amma ba yanzu ba, inji Hajiya Halima. Tace yanzu ko dan gida ne idan ba za'a bashi wani abu ba ba zai je yiwa mutum sako ba.
Hajiya Halima ta cigaba da cewa ko iyaye ne, uwa da uba, idan suna yawan aikan yaron sai ya soma ki sai dai da toshiya. Tace matsalar cin hanci tun daga gida ake farawa. Injita yanzu ya kamata a fara wayarwa jama'a kai su fahimtu da illar wannan muguwar dabi'a
Alhaji Abdullahi Ibrahim kwamishanan 'yansanda mai ritaya yayi bayanin yadda cin hanci ya samu asali a sashen 'yansanda. Yace wadansu ba'a daukansu aikin 'yansanda sai sun bada kudi. "Mai daukan kurtu da yace sai an bashi Naira dubu dari ya karfafawa kurtun gwuiwa ne da zara ya kama aiki sai ya soma karban nagoro", inji kwamishanan.
A jihar Gombe kuwa kungiyar Rasulul Azam ta wasu 'yan shiya ce ta gudanar da taron kasa akan zaman lafiya. Shaikh Sale Zaria sakataren kungiyar na kasa da Rebarend John Salem Tula daga bangaren kirista, kowannensu ya gabatar da jawabi akan mahimmancin zaman lafiya da juna.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.
Facebook Forum