A dai-dai lokacin da kungiyoyi masu zaman kansu, da wadansu masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, ke cigaba da fafutukar gani an ceto daliban Chibok, wadanda yau suke cikin kwanaki 170 a hannun wadanda suka sace su, Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya sha alwashin gani an kawo karshen ta’addanci a Najeriya.
Mr. Jonathan ya bayyana hakan ne a jawabinsa ga al-ummar kasa, dangane da cikar Najeriya shekaru 54 da samun ‘yancin kai.
Goodluck Jonathan yace babu dare babu rana, hukumomin tsaronmu na tunkarar ‘yan ta’adda, kuma samun gagarumin nasara.
Jonathan ya kara da cewa a matsayinsa na shugaba, zai dauki matakan da suka dace domin gani an murkushe ‘yan ta’adda, saboda haka yake kira ga ‘yan kasa su bada hadin kai, da hadin gwiwa wajen cimma matsala ba tare da nuna ban-banci ba.
“Duk da kalubalen tsaro da Najeriya ke fama da shi, an samu cigaba a fannin bunkasar tattalin arziki, da aikin gona, da matsalar yunwa a Najeriya”, fassarar kalamun Goodluck Jonathan.