'Yan hamayya a majalisar wakilai ta tarayya suna zargin gwamnatin tarayya da neman a yi rufa rufa kada 'yan majalisa dokokin kaa suyi muhawara ko bincike kan badakalar kudade dalar Amurka fiyeda milyan tara da aka jami'an Afirka ta kudu suka kama cikin 'yan makonnin nan.
Idan ba'a manta ba jami'an tsaro a Afirka ta kudu sun kama jirgin sama mallakar shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya Pastor Oritsejafor da kudi dala milyan 9.3 da wasu 'yan Najeriya biyu da ba yahude daya.
Bayanan da suka fito daga hukumomin Najeriya shine cewa, da sanin gwamnatin tarayya aka yi balaguron wai da nufin sayen makamai. Wannan batu ya janyo muhawara a duk fadin kasar da har yanzu ba a daina. Kungiyoyi da daidaikun jama'a suna ta kira ga gwamnatin Najeriya tayi bayani kan wannan batu.
Ranar Talata majalisar wakilai ta tarayya ta nemi a yi muhawara kan wannan batu, amma 'yan hamayya sun yi zargin cewa an hana su ta wajen kin bin sharuddan tafiyar da aikin majalisa.
Ahmed Babba-kaita yana daga cikin 'yan hamayya a inuwar APC da suka fice daga zauren majalisa kuma ya yiwa