Shugabannin addinan na arewa maso gabas sun ce akwai bukatan 'yan siyasa suyi takatsantsan su sa akidar yiwa jama'a aiki a gabansu.
Wakiliyar Muryar Amurka tayi fira da Shaikh Isa Tali Yawa na addinin muslunci da Rabaran Abari Kalla na addinin kirista. Shaikh Isa Tali yace suna kiran 'yan siyasa su zama masu tunani, masu hangen nesa a lamarin masalaha da kuma cigaban kasar. Su fifita bukatun cigaban Najeriya da al'ummarta akan bukatunsu na kansu.
Shaikh Isa yace a dubi zamanin marigayi Sardauna da Tafawa Balewa yadda suka rungumi kasa da adalci da tunani mai kyau na hada kan kowa da kowa. Sun hada 'yan kudu da arewa sun zama daya. Domin basu fifita kansu ba fiye da kasar yasa har yanzu ba'a manta dasu ba. Sabili da haka ana kiran 'yan siyasa su fifita son bukatar al'ummarsu akan nasu bukatun. Fifita bukatar kai fiye da na kasa da al'umma shi zai sa a cigaba da fafata fada. Kafin a zauna lafiya sai kowa ya so wa dan'uwansa abun da yake so ma kansa.
Shaikh ya kira masu son hawan mulki da wadanda suke kai yanzu su yi dogon tunani a cikin lamuransu su dubi matsalar al'umma su tsaya cikin natsuwa da tsoron Allah domin ya zabar ma kasar abun da yafi mata alheri.
Shi ma Rabaran Abari Kalla ya kira 'yan siyasa su maida hankali domin yija ba yau ba ce domin kawunan mutane na dada wayewa. Lokutan baya can danniya tayi yawa. Son zuciya yasa sukan dorawa mutane nasu dan takarar ba tare da son talakawa ba. Su yi hankali su bar talaka yace ga wanda yake so. Duk mai yin adalci a mulki ba sai ya nemi ya dawo ba. Jama'a da kansu zasu nemi su dawo. Wadanda basu yi abun kirki ba kada su sake cusa kansu dole sai an zabesu domin suna da kudin sayen mutane da kuri'u. Idan sun yi haka nan gaba ba zasu samu lafiya ba. Yakamata a yi zaben a cikin salama da kuma lafiya a kananan hukumomi da jihohi domin cigaban kasar.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.