A lokacin da ya ke jawabi wajen kaddamar da shirin tallafa wa matasa da ake kira P-YES a takaice a birnin tarayya Abuja, wanda aka kirkira da zimmar samar da ayyuka 774,000 a kananan hukumomin da ke fadin kasar, Shugaba Buhari ya kuma bada umarnin cewa a hukunta duk wadanda ke da hannu wajen yin ba daidai ba.
“Zan yi amfani da wannan damar don in yi bayani akan yadda 'yan Najeriya suka nuna damuwa kwanan nan game da yadda wasu jami'an 'yan sanda ke amfani da karfi da kashe-kashe ba bisa ka'ida ba da kuma yin wasu abaubuwa marasa kyau,” abinda Shugaba Buhari ya fada kenan a lokacin bikin kaddamar da shirin na P-YES, wanda ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo, da Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan, da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da kuma Injiniya Dave Umahi na jihar Ebonyi.
Shugaba Buhari ya kara da cewa “soke rundunar SARS shine mataki na farko na kudurin yin gagarumin garambawul a tsarin ‘yan sandan kasar don a tabbatar cewa babban aikin su da sauran jami’an tsaro zai ci gaba da kasancewa na kare rayuka da rayuwar al'uma.
A game da shirin samar da ayyuka, Shugaban, a yayin da ya ke sake nanata ci gaba da kudirin gwamnatinsa na bunkasa rayuwar matasa da kuma kawar da talauci ya yi alkawarin cewa manufofin gwamnatin tarayya na kare rayuwar al’uma da tallafa musu za su ci gaba kamar yadda aka fara, duk da kalubalen da annobar COVID-19 ta haifar.
Facebook Forum