Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Soke Rundunar 'Yan Sandan SARS a Najeriya


Wani dan sandan Najeriya
Wani dan sandan Najeriya

Babban Sufeto Janar din ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu, ya soke runduna ta musamman da ke yaki da masu fashi da makami wacce ake kira SARS a takaice.

Wannan mataki na zuwa ne bayan jerin zanga zangar da wasu manyan biranen Najeriya suka fuskanta inda ake zargin rundunar ta SARS da cin zarafin mutane, a wasu lokuta ma har da kisa, zargin da rundunar ke musantawa.

Sufeton na ‘yan sanda ya bayyana daukan wannan mataki ne a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja a ranar Lahadi Bayan wane taro da manyan jami'an 'yan sanda suka yi.

Gabanin soke rundunar, Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Prof. Yemi Osibanjo sun gana da sufeto Janar na ‘yan sandan.

Wannan shi ne karo na biyu cikin kwana guda da shugaba Buhari ya gana da IGP Adamu domin neman bakin zaren warware matsalar da ke damun ‘yan Najeriya game da cin zarafi da ke karuwa a fadin kasar.

Bayan tattaunawar tasu shugaba Buhari ya wallafa a shafin Twitter cewa “na sake ganawa da sufeto janar na ‘yan sanda a yau. Kudurinmu na sake fasalin hukumar ‘yan sanda babu shakka cikinsa. Ina samun bayanai akai-akai kan yunkurin da ake na samar da sauyin da zai kawo karshen cin zarafin da ‘yan sanda su ke yi da rashi da’a.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG