Domin ganin an cimma kwakkwaran daidaito da kuma zaman jituwa mai dorewa tsakanin kabilar Fulani da sauran kabilun Najeriya, kungiyar Miyetti Allah ta kasa ta sake jaddada cewa babu kanshin gaskiya a zargin da ake na cewa Fulani zasu kai hari jihohin kudu maso gabashin kasar.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah a yankin kudu maso gabas, Alhaji Gidado Sadique ya musanta maganganun dake cewa wasu Fulani zasu zo su kai hari jihohin Anambra da Enugu. Ya ce a nasu binciken babu wata matsala tsanin Fulani da jihohin biyu. Amma ya ce suna tsoron kada wasu su yi wani abu a dauka Fulani ne suka yi. Ya ce dalili ke nan da suka tashi suka karyata zargin
Dangane da matakan da yakamata a dauka wajen magance rikice-rikicen da kan barke tsakanin Fulani da wasu a kasar, Alhaji Muhammadu Njibdo Tugga, wani shugaban al’umma a yankin, ya ce a kafa wani kwamiti mai karfi da zai shiga tsakanin Fulani da kabilun da suke zaune cikinsu domin a shawo kan yawan barkewar rikici.
Yanzu dai, akwai alamun cewa ba za'a bar maganar ta mutu ba, kamar yadda Mista Hosea Karma, mataimakin sufeto janar na 'yan sanda mai kula da rundunar ‘yan sandan yankin. Injishi kodayake basu ji ba zasu gudanar da cikakken bincike akan lamarin.
A saurari rahoton Alphonsus Okoroigwe
Facebook Forum